Kungiyar farautar masu manyan laifuffuka ta kasa da kasa, Interpol ta yi alkawari a ranar Litinin na kara rubunya ayyukanta domin cafke masu laifin dake gudu da ake zargi da hannu kan kisan kiyashin shekarar 1994 a kasar Rwanda.
Babban sakatare na kungiyar Interpol, Ronald Kenneth Noble ya yi wannan furuci a yayin bude taron kwararru kan kisan kiyashi, laifuffukan yaki da manyan laifuffukan keta hakkin bil'adama karo na shida dake gudana a yanzu haka a birnin Kigali bisa taken "kawo karshen rufe ido kan laifi".
Ba za'a damu da tsawon lokacin da wannan aiki zai dauka, Interpol ba za ta huta har sai ta cafke dukkan masu laifin dake gudu, kuma akwai hadadiyyar dangantaka mai kyau tsakanin kasashe da za ta taimaka waje cafke wadannan mutane, in ji mista Noble. (Maman Ada)