in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rwanda ta yi bukin cika shekaru 20 na kisan kiyashin jama'a a kasar
2014-04-08 12:37:48 cri

A ranar Litinin ne kasar Rwanda ta fara gudanar da wadansu shirukka, domin tunawa da zagayowar ranar cika shekaru ashirin cif, na kisan kiyashin da aka yi a kasar, inda aka hallaka 'yan kabilar Tutsi kimanin dubu 800.

An dai yi tsit na minti guda a duk fadin kasar, har da kafofin watsa labarai na radiyo da talabijin dake kasar, a inda kuma aka saukar da tutar kasar domin jimamin wannan rana.

Shugaban kasar ta Rwanda Paul Kagame, a yayin bukin tunawa da wadanda suka rasa rayukansu, a wani kisan kiyashin 'yan kabilar Tutsi dubu 300 da aka yi a shekara ta 1994, a tsaunin Gisozi, wanda ke kallon birnin na Rwanda, ya kone wata wuta da aka yiwa lakabi da "hasken fata na gari", wacce za ta ci gaba da kasancewa a kone har zuwa watan Yuli.

Shi dai wannan bukin zagayowar ranar kisan gillar 'yan kabilar ta Tutsi, an yi masa taken "Tunawa, hada kai, da sabunta girmama jimamin wadanda suka rasa rayukansu, tare da samar da tudun dafawa ga wadanda suka tsira daga kisan kiyashin kabilar Tutsi na shekara ta 1994". (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China