FIFA ta ce 'yan kasar Brazil ne ke kan gaba wajen sayen tikitin, inda suka sayi sama da tikiti miliyan guda. Sai kuma Amurkawa da suka sayi tikiti 154,000, yayin da kuma 'yan kasar Australia suke biye da yawan tikiti 40,000.
'yan kallo daga Kasar Birtaniya sun sayi tikiti 38,000, yayin da na kasar Colombia suke sayi tikiti 33,000.
Zangon sai da tikitin na wannan lokaci dai zai kare ne ran 1 ga watan Afirilu, ana kuma fatan bude zango na karshe a ranar 15 ga watan na Afirilu.
Don gane da wasannin da aka saye tikitin su kuwa, FIFA ta ce yanzu haka, babu sauran tikitin wasanni 13, da za a buga a biranen Rio de Janeiro, da kuma Sao Paulo.
Haka nan an sayar da dukkanin tikitin wasannin Jamus da Portugal, wanda za a buga a Salvador, ranar 16 ga watan Yuni, da wasan Italiya da Uruguay a Natal, na ranar 24 ga watan na Yuni. Da ma wasan Ingila da Italiya a Manaus, na ranar 14 ga watan Yuni. (Saminu Alhassan)