Shugaban kasar Senegal Macky Sall da takwaransa na kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita sun dauki niyyar karfafa dangantakarsu ta fuskar tsaro, musammun ma wajen yaki manyan laifuffukan kasa da kasa, a cewar wata sanarwar da ta biyo bayan karshen ziyarar kwanaki biyu da shugaban kasar Mali ya kai birnin Dakar.
Dangantakar tsaron za ta tabo musammun ma batun yaki da ta'addanci, ta hanyar gudanar da sintirin hadin gwiwa tsakanin jami'an tsaron kasashen biyu, in ji wannan sanarwa. A gaban tashe-tashen hankali da yake-yake dake faruwa a wasu yankunan nahiyar Afrika, da karuwar ayyukan ta'addanci a yankin Sahel, kasashen Mali da Senegal sun bayyana damuwarsu ta hanyar yin kira ga zaman lafiya, zaman karko da hadin kan al'ummar kasashen nahiyar Afrika.
A wasu fannoni, in ji sanarwar, shugabannin biyu sun jaddada niyyar matuka wajen bunkasa noma da kuma ingiza kasashen biyu zuwa matsayin koli. (Maman Ada)