Shugaban kasar Senegal Macky Sall ya sanar a ranar Laraba a birnin Dakar da taron fadada shawarwari ga jam'iyyun siyasa da kungiyoyin fararen hula kan shirin gyaran fuskar kasa kan mataki na uku na tsarin rarraba mulkin kasa.
Mista Sall ya yi wannan furuci bayan sallar Aid el Kebir da aka sani da sallar layya a kasar Senegal a babban masallacin dake birnin Dakar.
A cikin hudubarsa, limamin masallancin El Alioune Moussa Samb ya mai da hankali kan hadin kan 'yan kasa da muhimmanin zama tsintsiya madaurin daya game da muhimman abubuwan cigaban kasa.
A cewar shugaban kasar Senegal, wannan na zuwa ne daidai da kiran da ya yi na cimma ra'ayi guda kan gyaran fuskar fadin kasa. 'Na yi kira a 'yan kwanakin da suka gabata da ya kamata a aiwatar tun daga mako mai zuwa ta hanyar fadada yin shawarwari kan wannan muhimmin batu na sake gyara tsarin hukumomin kasa, rarraba tsarin mulkin yankuna, baiwa jama'a damar tafiyar da harkokin yankunansu da kuma cigaban yankuna.' in ji Macky Sall.
Bisa wannan shiri, shugaban kasar Senegal na bayyana niyyarsa ta hada jam'iyyun siyasa, kungiyoyin fararen hula da kuma wakilan jama'a domin kowa ya tofa albarkacin bakinsa kan muhimman batutuwan da suka shafi kasa. (Maman Ada)