in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Senegal ta kaddamar da wani shirin rubuta tarihin kasar baki daya
2014-03-31 10:07:30 cri

Kasar Senegal ta kaddamar da wani shirin rubuta tarihin kasar baki daya a kwanan nan a birnin Dakar a karkashin jagorancin malaman jami'o'i, marubuta, masana, malaman addinai, 'yan wasa, 'yan jarida, masanan shari'a da kuma masanan tarihi na kasar.

Malamin jami'a kuma 'dan siyasar kasar Senegal Iba Der Thiam ya bayyana a yayin wannan taro cewa, burin da ake son cimma wa shi ne na rubuta tarihin Senegal baki daya da zai yi la'akari da hakikanin gaskiyar al'ummar kasar, kuma zai shiga cikin tarihin shiyyar da kasar Senegal take ciki, bisa yanayin Afrika, haka ma tare da la'akari da tarihin duniya. Kundin da aka rubuta za'a raba shi zuwa kashi kashi, kuma za'a fassara shi zuwa sauran harsunan kasar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China