Mista Ladsou ya yi wannan furuci a ziyarar da ya kai a Juba, babban birnin Sudan ta Kudu, inda ya samu ganawa tare da shugaba Salva Kiir, in ji kakakin MDD, Martin Nesirky a yayin wani taron manema labarai.
"Mista Ladsou ya jaddada cewa abu na farko shi ne aiwatar da yarjejeniyar dakatar da bude wuta da tashe-tashen hankali da aka cimma a ranar 23 ga watan Janairu. Haka kuma ya bayyana goyon bayan MDD kan shiga tsakanin da kungiyar IGAD take wajen ganin an kawo karshen rikicin Sudan ta Kudu," in ji mista Nesirky.
A karkashin shiga tsakanin IGAD, gwamnatin Sudan ta Kudu bisa jagorancin Salva Kiir tare da 'yan tawayen dake biyayya ga tsohon mataimakin shugaban kasa Riek Machar sun amince a ranar 23 ga watan Janiaru na su kawo karshen zubar da jini a cikin kasarsu. (Maman Ada)