Firaministan kasar Libya Abdullah Al-Thinni, ya mika takardar barin aiki ga majalissar dokokin kasar, sakamakon barazanar da ya fuskanta a ranar Asabar. Al-Thanni wanda ya bayyana bukatar sa ta ajiye aiki a ranar Lahadi, ya ce, ba zai iya amincewa ya jefa rayuwar iyalinsa cikin hadari ba.
Kafofin yada labarun kasar sun labarta cewa, a daren ranar Asabar ne wasu tsageru dauke da muggan makamai, suka yiwa unguwar da firaministan ke zaune da iyalinsa tsinke, suka kuma yi masa barazanar lallai ya sauka daga mukamin nasa.
Ba a dai kai ga tantance ko su waye tsagerun da suka yiwa firaminstan barazanar ba. Halin da ake ciki dai ya nuna cewa, Thinni ba zai jagoranci kafuwar sabuwar gwamnatin kasar ba.
Shi dai Al-Thinni ya maye gurbin Ali Zeidan ne a matsayin firaministan wucin gadin kasar na 'dan lokaci a watan jiya, an kuma tsara sabunta wa'adin aikinsa bayan dukkan makonni biyu-biyu. Sai dai a baya bayan nan majalissar dokokin kasar ta fada rudani, kan batun wanda zai maye gurbin mukamin na firaminista, kafin kuma a ranar Talata a umarci Thinni, da jagorantar kafa sabuwar gwamnati cikin mako guda. (Saminu)