in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bukaci firaministan Libya da ya kafa sabuwar gwamnati
2014-04-09 12:53:59 cri

Majalisar dokokin kasar Libya a ranar Talata ta umurci firaministan kasar mai rikon kwarya, Abdullah al-Thinni da ya ci gaba da rike akalar gwamnatin kasar ta Libya, amma a bisa sharadin sai ya kafa gwamnati a cikin mako guda.

Wani kakakin majalisar dokokin kasar ya bayyana cewar, wakilan majalisar sun umurci firaministan da ya rike mukaminsa, har sai an zabi 'yan majalisar wakilai ta Libya, a inda ya kara da cewar, babbar majalisar hadin kai ta kasar Libya, wacce ita ce hukuma mafi karfin iko a siyasance a kasar, ta zartas da umurni na tilasatawa wakilan gwamnatin kasar na yanzu, yin murabus daga kan mukamansu, a inda kuma suka bukaci al-Thinni da ya maye gurbinsu da sabbin jami'ai.

A watan jiya ne, babbar majalisar hadin kai ta kasar ta kawar da tsohon firaministan kasar Ali Zeidan, daga mukaminsa, a inda kuma sai babbar majalisar ta nada tsohon ministan tsaro na kasar al-Thinni a matsayin firaminista mai rikon kwarya.

Ita dai babbar majalisar hadin kai ta kasar Libya tana sabunta wa Abdullah al-Thinni ikon tafiyar da gwamnatin kasar a bayan kowane makonni biyu.

A halin da ake ciki dai majalisar hadin kan kasar ta Libya ta shiga halin kaka-nika-yi a yayin da ta kasa zaben wanda zai maye gurbin Zeidan, tsohon firaministan kasar da'a aka cire.

Kasar dai ta Libya ta shiga wani hali na gwaggwarmayar kama madafun iko, tsakanin kungiyoyi dake da sha'awar a dama da su a gwamnati, musamman bayan rikicin shekarar ta 2011, wanda ya yi sanadiyyar kawar da gwamnatin tsohon shugaban kasar ta Libya Muammar Gaddafi. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China