An rantsar da tsohon ministan tsaro kasar Libya, Abdullahi al-Thani, a matsayin firiministan kasar na wucin gadi. A jiya Talata, aka rantsar da shi a inda hakan ya ba shi damar gudanar da mulki na wucin gadi.
Tun farkon jiyan, majalisar dokokin Libyar ta gabatar da sunan tsohon ministan tsaron a matsayin firaministan kasar na wucin gadi, bayan da tsohon firaministan kasar ya rasa mukaminsa, sakamokon jefa kuri'ar rashin amincewa.
Shi dai sabon firaministan na rikon kwarya Abdullahi Thani zai rike kasar tsawon makonni biyu, har kafin a samu wanda zai maye gurbin tsohon firaministan kasar Ali Zeidan.
An dai sauke Zeidan ne a dalilin rikici tsakanin hukumomin kasar da kuma kabilun kasar masu fada a ji, dake yankunan gabashin kasar, saboda takaddamar fitar da man fetur din kasar zuwa kasashen ketare.
An dade ana caccakar gwamnatin Zeidan saboda ta kasa rike kasar, dake arewacin Afrika tun bayan shekaru kusan arba'in da Muammar Gaddafi ya yi yana mulkin kasar. (Suwaiba)