Mahukuntan kasar Nijar sun mika wasu manyan jami'an hambararriyar gwamnatin shugaba Ghaddafi na Libya zuwa kasarsu. Wata majiya daga ofishin jakadancin kasar ta Libya dake Nijar, ta tabbatar da damka mutanen su 10 ga mahukuntan Libya a ranar Laraba.
Cikin watan Maris da ya gabata ma dai sai da mahukuntan kasar ta Nijar, suka mika 'dan tsohon shugaba Gaddafi, wato al-Saadi Gaddafi, shi da tsohon shugaban hukumar tsaron farin kaya ta kasar Abdullah Mansour gida domin su fuskanci shari'a. Bayan da Nijar din ta zarge su da karya ka'idar mafakar da ta ba su.
Hakan kuwa ya biyo bayan zargin da Libya ta yi cewa, mutanen biyu na kokarin shiryawa sabuwar gwamnatin kasar juyin mulki. Daga bisani Saadi Gaddafi ya amsa laifin shirya hargitsin da ya auku a Sebha, dake kudancin kasar ta Libya, lamarin da ya haddasa rasa rayuka, da raunata mutane da dama.
Akwai dai jami'an tsohuwar gwamnatin Libya da dama dake samun mafaka a kasar ta Nijar, biyowa bayan juyin mulkin watan Oktobar shekarar 2011, wanda ya kawo karshen gwamnatin shugaba Gaddafi. (Saminu)