in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika ta Kudu za ta zuba jarin dalar Amurka biliyan biyar a fannin layin dogo
2013-10-20 16:18:58 cri
Gwamnatin kasar Afrika ta Kudu ta sanar a ranar Asabar cewa tana shirin zuba jarin dalar Amurka biliyan biyar a harkokin sufurin layin dogo a cikin shekaru masu zuwa.

Shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma ya yi wannan furuci a yayin bikin kaddamar da shirin Bridge City Rail Project a birnin Durban.

Mutane da dama na amfani da jiragen kasa wanda ya kasance muhimmin fanni a cikin harkokin yau da kullum na jama'a, in ji shugaba Zuma.

Tsarin layin dogo a kasar Afrika ta Kudu ya kasance wanda ya fi samun ci gaba a nahiyar Afrika, kuma dukkan biranen kasar suna hadewa ta hanyoyin layin dogo domin haka sufurin jiragen kasa muhimmin jigo ne ta fuskar jigilar jama'a, dalilin haka ne ya kamata mu ci gaba da zuba jari a wannan fanni, in ji mista Zuma.

A tsawon shekaru biyar na baya bayan nan, gwamnatin Afrika ta Kudu ta zuba dalar Amurka biliyan hudu a cikin gine-ginen ababen more rayuwa da na ayyukan layin dogo, har ma da jiragen kasa masu gudun fitar hankali. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China