A kasar Zimbabwe, hukumar haraji ta kasar ta gabatar da shirin tsaurara matakan sanya ido kan harkokin kudi a kasar domin kawar da matsalar ficewar makudan kudade daga kasar.
Babban jami'in hukumar haraji ta kasar Zimbabwe, mista Geshorn Pasi ya bayyana cewa, kasar tana fama da matsalar ficewar kudade masu tarin yawa. Kasar tana amfani da kudaden kasashe waje a halin yanzu, dalar Amurka ita ce aka fi amfani da ita a cikin kasar, kuma a matsayin kudin misali da na hada hada.
Mista Pasi ya shaida wa wani kwamitin 'yan majalisu a ranar Talata cewa, hukumarsa ta gabatar da wasu matakai ga gwamnatin kasar domin magance matsalar ficewar kudade. A halin yanzu, mutumin kasar Zimbabwe guda na iyar fita daga kasar da dalar Amurka dubu goma a ko wace tafiya ba tare da an takaita yawan balaguron ba, domin haka ne kudade da dama suke fita daga kasar, in ji jami'in. (Maman Ada)