in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta jaddada azamarta ta kara tallafawa cigaban Zimbabwe
2013-11-27 12:00:21 cri

MDD za ta samar da karin taimako ga cigaba a maimakon tallafin jin kai ga kasar Zimbabwe da zummar tallafawa kokarinta na bunkasa tattalin arzikin kasar, in ji wani babban jami'in gwamnatin kasar a ranar Talata.

Mataimakin sakatare janar a fadar shugaban kasar Ray Ndhlukula ya bayyana cewa, ba da tallafi ga samun cigaba zai taimakawa kasar Zimbabwe wajen bunkasa tattalin arzikin da takunkumin kasashen duniya ya kawo mata.

Haka kuma ya bayyana cewa, bangarorin biyu sun amince da rage ayyukan jin kai domin maye gurbinsu da wasu ayyukan cigaban kasa.

Mista Ndhlukula ya yi wannan kalami ne a yayin wani taron da ya shafi nazari kan tsarin taimako ga cigaban Zimbabwe na MDD da aka fara daga shekarar 2012 har zuwa shekarar 2015.

Tsarin ya kasance wani jadawali na cigaba dake nuna hanya ga aikin dukkan cibiyoyin MDD dake kasar Zimbabwe.

Mai tafiyar da harkokin MDD a kasar Zimbabwe, Alain Noudehou ya bayyana a lokacin wannan taro cewa, kungiyoyin MDD sun fitar da dalar Amurka miliyan 426 domin tallafawa muhimman ayyukan cigaba na jama'a a kasar Zimbabwe a shekarar 2012. Jami'in ya kara da cewa, MDD za ta samar wa kasar Zimbabwe dalar Amurka miliyan 430 a shekarar 2013. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China