Mahukuntan kasar Kenya sun ce, sun tisa keyar 'yan kasar Somaliya 82 zuwa gida, a ci gaba da ake yi da daukar matakan dakile yaduwar ayyukan ta'addanci a kasar.
A ta bakin sakataren sashen tsaro cikin gida, na majalissar zartaswar kasar ta Kenya Joseph Ole Lenku, mutanen da aka mayar kasar tasu ta asali, sun shiga Kenya ne ba da izini ba, an kuma dauki matakan duk da suka dace da doka wajen mai da su kasar ta Somaliya.
Tun dai daga ranar 5 ga watan Afirilun nan ne jami'an tsaron Kenya suka matsa kaimi, wajen kame bakin haure dake zaune cikin kasar ba tare da cikakkun takardun shaidar izini daga hukumomin kasar ba. Matakin da a cewar Lenku ya dace da matakan shari'a. (Saminu)