in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An hallaka mutane 8 a kusa da kan iyakar Kenya da Somaliya
2013-12-11 10:48:16 cri

Mutane akalla 8 ne suka rasu, ciki hadda fararen hula su 3, bayan da wasu dakaru da ake zaton 'yan kungiyar nan ta Al-Shabaab ne suka bude musu wuta a garin Liboi, dake kusa da kan iyakar kasar Kenya da Somaliya.

Harin na ranar Talata 10 ga wata, a cewar kwamandan rundunar 'yan sandan Dadaab Kalicha Roba, ya auku ne a lokacin da wasu jami'an 'yan sanda su 5, suke gudanar da sintiri a yanki. Ya ce, maharan sun yiwa wadannan jami'ai kofar rago suka kuma bude musu wuta.

Da yake karin haske kan wannan batu a birnin Nairobin kasar ta Kenya, mataimakin babban sifeton 'yan sandan kasar mai lura da harkokin mulki Samuel Arachi, ya ce, akwai kuma wasu jami'an hukumar su biyu da suka bace sakamakon aukuwar wannan hari. Arachi ya kara da cewa, tuni rundunar ta fara farautar wadanda suka kaddamar da wannan hari, tare da kokarin gano jami'an da suka bata.

A nasa bangare, Musa Yego, wanda ke matsayin babban jami'in hukumar binciken manyan laifuka na gundumar Garissa, cewa ya yi, ba a kai ga tantance ko 'yan bindigar sun tsere da makaman jami'an 'yan sandan da suka harbe ba. Yego ya ce, wannan hanya ta Dadaab zuwa Liboi ta shahara wajen kaiwa jami'an rundunar ta 'yan sanda hari.

Wasu rahotanni na cewa, mai yuwuwa ne maharan su kasance 'yan gudun hijira masu biyayya ga kungiyar Al-Shabaab dake sansanin Dadaab. Ana kuma ta'allaka harin na baya bayan nan da wani dukan kawo wuka, da jami'an tsaro suka yiwa wasu wadanda ake zargi da kaiwa 'yan sanda hari a gundumar ta Garissa.

Wannan ne dai hari na baya baya, da aka kaiwa jami'an tsaron, tun bayan harin Westgate na birnin Nairobi da ya haddasa mutuwar mutane akalla 67, tare da jikkata wasu sama da 200.

Majiyar rundunar sojin kasar ta Kenya ta bayyana cewa, wannan yanki na Garissa na daya daga muhimman yankuna dake da tasiri matuka, wajen samar da tsaro ga yankunan dake kusa da gabobin ruwan kasar, da kuma lardunan arewa amso gabashin kasar. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China