in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta baiwa 'yan sandan kasar Sin lambar yabo
2014-04-09 15:42:45 cri

Tawagar musamman ta MDD da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Liberiya, ta baiwa 'yan sandan kwantar da tarzoma na kasar Sin su 140 lambar yabo, bisa akin da suke yi na shimfida zaman lafiya a kasar.

Yayin bikin da aka shirya a jiya Talata, a sansaninsu da ke birnin Greenville, shugabar tawagar ta wanzar da zaman lafiya, kuma wakiliyar musamman ta babban sakataren MDD Madam Karin Landgren, ta bayyana cewa, tawagar jami'an kwantar da tarzoma ta 'yan sandan kasar Sin sun cancanci yabon da aka yi musu, tare da godiya ga taimakon da suka baiwa Liberia, a fannin bunkasa zaman lafiya da tsaro.

Landgren ta ce 'yan sandan kasar ta Sin na da kwarewa, sun kuma sauke nauyin da ke wuyansu. Kaza lika sun gudanar da aikinsu yadda ya kamata a kan lokaci, matakin da ya sanya su samun karbuwa daga jama'ar wurin. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China