Wani jami'in hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya (HCR) ya tabbatar a ranar Talata cewa, ana binciken wasu hanyoyi domin sake tsugunar da wasu 'yan gudun hijira da a yanzu haka suke zaune a cikin sansanin 'yan gudun hijira na Dukwi dake kasar Botswana, bayan boren baya bayan nan na wadannan 'yan gudun hijira kan tabarbarwar halin zaman rayuwarsu a wannan wuri.
A cewar HCR, kasar Botswana ta karbi 'yan gudun hijira kimanin dubu uku da kuma masu neman mafaka da yawancinsu suka fito daga kasashen Somaliya, Namibiya da Zimbabwe.
Suna zaune a sansanin na Dukwi, inda gwamnatin kasar ta Boswana ta dauki nauyin ba su hidimar ba da ilimi da kiwon lafiya. (Maman Ada)