Mahukunta a kasar Botswana sun bayyana aniyar fara gudanar da wani shirin tattara bayanai kan cutar kanjamau a dukkanin fadin kasar.
Shirin da aka tsara gudanarwa daga 15 ga watan Janairun sabuwar shekara mai zuwa, zuwa 15 ga watan Maris, a cewar babban jami'in lura da shirin yaki da cutar ta kanjamau a kasar Mr. Mpho Mmelesi, zai mai da hankali ne ga batun zakulo dalilan yaduwar cutar, dama wuraren da ta fi yin illa, tare da ragowar batutuwan da suka shafi alakar cutar da harkokin jima'i, baya ga nazarin tasirin shirin ilmantar da jama'a hanyoyin kariya, da na tasirin shirye-shiryen ba da tallafin hana yaduwarta.
Yayin wannan shiri wanda shi ne irin sa na hudu da za a gudanar a kasar ta Botswana, Mmelesi ya ce, za a yi amfani da fasahar sadarwa ta zamani wajen tattara bayanai, a maimakon amfani da takardu da a baya suka rika haifar da jinkiri da kurakurai, dake rage nasarar shirin.
Mmelesi ya kara da cewa, sakamakon wannan shiri zai baiwa mahukuntan kasar damar fidda sabbin tsare-tsaren tunkarar kalubalen dake gabansu, don gane da yaki da wannan cuta a nan gaba, ya kuma baiwa 'yan kasar karin damar sanin matsayinsu, tare da sada su da shirye-shirye da cibiyoyin ba da shawarwari da magunguna da gwamnatin kasar ke tanada.(Saminu)