in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Botswana ta zama kasa mafi janyo hankalin jama'a a bangaren hakar ma'adinai a Afirka
2014-03-10 12:22:16 cri

Wasu masu bincike daga kasar Canada sun rattaba kasar Botswana a matsayin kasa ta farko a Afrika wajen janyo hankali a bangaren hakar ma'adinai.

Cibiyar Frase ta buga sakamakon a cikin bincikenta na baya-bayan nan na kamfanonin hakar ma'adinai, wanda aka tsara, domin duba dokokin dake kara kaimin, saka jari a bangaren binciken da samar da ma'adinai.

Daga cikin wuraren da ake samun ma'adinin daiman, Botswana ce ta kasance ta farko a duniya, daga nan sai jihar Ontario ta Canada da Namibia.

Shi dai wannan bincike na shekara ta 2013, an rarraba shi ga manajoji da shugabannin kamfanonin haka 4100, tare da habaka ma'adinai.

Binciken dai ya gabatar da tambayoyi ga jama'a, a inda aka tambaye su a kan yadda dokoki da manufofi 15 da suka yi tasiri wajen yanke hukuncin, shawarar kamfani a game da saka jari, a bangarori da dama duk kuwa da kasancewar kalubale. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China