Kwamitin tsaron MDD ya yi Allah wadai, da kisan wasu jami'an dake aiki a ofishin yaki da fataucin kwayoyi na majalissar a kasar Somaliya. Har ila yau kwamitin ya yi kira ga mahukuntan kasar da su dauki matakan gaggauta hukunta wadanda suka aikata wannan danyen aiki.
An ce, jami'an biyu da suka hada da 'dan kasar Birtaniya daya, da kuma 'dan kasar Faransa daya sun gamu da ajalinsu ne, sakamakon bude musu wuta da wasu mahara su biyu suka yi, a wani wuri kusa da ofishin jami'an shige da fice dake filin jirgin saman Galkayo. Suna kuma kan hanyarsu ne ta halartar wata ganawa, da wasu jami'an kasar ta Somaliya, domin tattaunawa kan takaitaccen tsarin musayar kudade, wanda ya maye gurbin cikakken tsarin banki a kasar.
Tuni shi ma babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya la'anci kisan jami'an biyu, yana mai kira da a gudanar da bincike kan lamarin ba tare da wani bata lokaci ba. (Saminu)