in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in MDD ya yi kira da daukar karin matakan sake ginin Somaliya
2014-03-12 15:59:08 cri

Wakilin musamman na babban magatakardar MDD a kasar Somaliya Nicholas Kay, ya yi kira ga kwamitin tsaron majalissar da ya dauki karin matakan shawo kan kalubalen dake addabar kasar.

Kay, wanda ya yi wannan kira yayin da yake tsokaci ga mambobin kwamitin ta kafar talabijin daga birnin Mogadishu, ya ce, birnin na Mogadishu dake matsayin helkwatar kasar ta Somaliya, na matukar bukatar agajin kasashen duniya, wajen magance matsalar karancin tsaro.

Cimma wannan buri, a cewar sa, abu ne mai yiwuwa, matakin da kuma zai sharewa kasar damar fidda kudin tsarin mulki da kowa zai amince da shi, tare da gudanar da babban zaben kasar, da ma burin habaka tsaro nan da shekara ta 2016.

Wakilin musamman na babban magatakardar MDDr ya kara da cewa, tsaro shi ne babban kalubale ga aikin da ake fama da shi a Somaliya, kasancewar 'yan tada kayar baya na ci gaba da gudanar da hare-hare a baya bayan nan a sassan kasar daban daban, musamman kan faraen hula, da jami'an MDD, da ma uwa uba fadar shugaban kasar.

Don gane da matakan da ake dauka kuwa, Kay ya ce, tawagar AMISOM, da ta kasar Somaliyan SNA, na iyakacin kokarin dakile ayyukan 'ya'yan kungiyar Al-shaab, wadda a shekarar 2011 da ta gabata, aka samu nasarar korar ta daga babban birnin kasar. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China