in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi suka ga mummunan harin da aka kai a ofishin 'yan sanda a Somaliya
2013-11-20 10:56:26 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon ya yi suka da kakkausar murya game da mummunan harin da aka kai a ofishin 'yan sanda a kasar Somaliya, yana mai cewa, ayyukan 'yan ta'addan suna kawo manyan wahalhalu ga jama'a.

A cikin wata sanarwa da kakakin majalissar ya fitar ya ce, Mr. Ban ya soki wannan mummunan harin a kan ofishin 'yan sanda a Beledweyne na kasar Somaliya, abin da ya biyo bayan hare-hare da dama a 'yan makonnin nan.

Sanarwar ta ce, wadannan irin hare-hare a kan gwamnati da al'ummar Somaliya suna saka jama'a cikin wani hali na tashin hankali matuka.

Wata mota mai dauke da bam da wani 'dan kunar bakin wake ya tuka ne ya kai hari a bakin kofar ofishin 'yan sandan a tsakiyar garin Beledweyne na Somaliya wanda nan ne babban birnin yankin Hiran, cibiyar kasuwanci da ya hada arewaci da kudancin Somaliya.

Beledweyne dai yana da nisan kilomita 300 daga arewacin Mogadishu, kuma nan ne cibiyar 'yan Djibouti dake aikin wanzar da zaman lafiya na kungiyar tarrayar Afrika AU da ake kira AMISOM. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China