A cewar Godana Doyo, gwamnan yankin Isiolo, wani rahoto daga hukumar yaki da fari ta kasar Kenya ya sheda cewa, muddin aka gaza daukar matakai cikin gaggawa, jama'ar da yawansu ya kai fiye da dubu 200 wadanda ke zama a yankunan Marsabit, Isiolo, da Wajir za su fuskanci matsalar yunwa.
Gwamna Doyo ya ce fari mai tsanani ya tilasta wa makiyayan arewacin kasar kaura zuwa kasashe makwabta don samun abinci, ruwa, da ciyayin da dabbobi suke bukata. Sai dai yadda aka yi kaura tare da dabbobi ya sa aka fara fama da karancin madara a wannan wurin, lamarin da ya tsananta yanayin tamowar da yaran wurin suke fama da ita. Rahoton hukuma ya ce ya zuwa yanzu matsalar ta ritsa da fiye da kashi 17 cikin 100 na yaran wurin. (Bello Wang)