Shugabannin kungiyar tattalin arzikin yammacin Afrika ECOWAS sun cimma wata yarjejeniya da za ta ba da damar gina hanyar da za ta tashi daga Abidjan na kasar Cote d'Ivoire zuwa birnin Lagos a tarayyar Najeriya, in ji kwamitin kungiyar ECOWAS a ranar Laraba a cikin wata sanarwa.
Shugabannin Najeriya, Benin, Cote d'Ivoire, Ghana da Togo suka sanya hannu kan wannan yarjejeniya a yayin taron baya bayan nan karo na 44 na shugabanni da gwamnatocin kungiyar ECOWAS a Yamoussoukro na kasar Cote d'Ivoire, a cewar sanarwar da Sunny Ugoh, kakakin kwamitin kungiyar ECOWAS ya sanya wa hannu a birnin Abuja.
Yarjejeniyar ta bukaci kasashen biyar da su gina tare da kulawa da babbar hanyar da ta kunshi hanyoyi shida, tare kuma da kafa wata hukumar da za ta dauki nauyin kulawa da wannan hanya bisa matsayin musamman na kasa da kasa, in ji sanarwar tare da bayyana cewa, wannan shiri zai taimaka wajen kawo sauki wajen jigilar jama'a da kayayyaki yadda ya kamata cikin wannan shiyya.
Kasashen biyar tuni sun yi alkawarin zuba dalar Amurka miliyan hamsin domin gudanar da shirye shiryen ayyukan wannan aiki dake janyo hankalin manyan masu zuba jari, haka kuma aikin zai shafi kashi 70 cikin 100 na kai da kawon harkokin kasuwanci a yankin ECOWAS. (Maman Ada)