Ministocin kungiyar kasashen tattalin arzikin yammacin Afrika ECOWSA na gudanar da wani zaman taron musamman a ranar yau Alhamis a birnin Abidjan na kasar Cote d'Ivoire domin tattauna shirin kawo gyaren fuska kan wannan hukuma. Sanarwar ta fito ta bakin shugaban kwamitin ECOWAS, mista Desire Kadre Ouedraogo bayan wata ganawarsa a ranar Talata tare da shugaban kasar Cote d'Ivoire Alassane Ouattara kuma shugaban kungiyar ECOWAS a wannan zagaye.
Zaman taron na musamman na kwamitin ministocin kungiyar zai tattauna game da shirin kawo sauye-sauye a wannan babbar hukuma ta shiyyar yammacin Afrika kamar da yadda babban taron kungiyar ECOWAS karo na 43 ya tanada, in ji mista Kadre Ouedraogo.
A karshen wani zaman taron da aka shirya a birnin Abujan Najeriya cikin watan Yulin shekarar 2013, an dauki matakin kara yawan ma'aikatan kwamitin, bisa misali adadin kwamishinonin dake a halin yanzu guda 9 za'a kai zuwa 15, haka kuma taron zai mai da hankali kan sauran wasu batutuwa da suka jibanci tafiyar da aikin wannan kungiyar ta ECOWAS, in ji mista Kadre Ouedraogo a gaban menama labarai. (Maman Ada)