A yau ne wakilin kasar Sin na musamman kan batun Gabas ta Tsakiya, Wu Sike zai halarci wani taron ministoci a kasar Italiya a kan batun samarwa kasar Libya taimako daga kasashen duniya.
Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Qin Gang ya ce, Wu Sike, zai kuma kai ziyara ga kasar Palasdinu da kuma Isra'ila daga yau, tare da kammala ziyararsa a ranar 12 ga watan na Maris.
Kakakin ya kara ada cewa, Mr.Wu zai yi musayar ra'ayi da bangarorin da suka dace a game da kara gina tattalin arziki da na rayuwa na kasar Libya, da kuma halin da ake ciki na tattaunawar samar da zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Palasdinu, tare da duba yanayin yankin na Gabas ta Tsakiya. (Suwaiba)