Manzon musamman na kasar Sin mai kula da harkokin yankin Gabas ta Tsakiya, Wu Sike, ya yi kira ga al'ummomin kasa da kasa da su duba yiwuwar samar da agajin jin kai ga kasar Libya, ta hanyar martaba cikakkun yankunanta, 'yancinta da kuma hadin kan kasar.
Mr. Wu ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga taron ministoci a kasar Italiya game da samar da taimakon kasa da kasa ga kasar ta Libya.
Jami'in na kasar Sin ya kuma yabawa kokarin kasar ta Libya da kuma irin ci gaban da aka samu a bangaren shirin mika mulki da farfado da tattalin arzikin kasar. Sannan ya bayyana kudurin MDD na taka rawar da ta dace wajen sake gina kasar.
Bugu da kari a wannan rana ce firaministan kasar ta Libya Ali Zeidan, ya gana da Mr. Wu a kasar ta Italiya, inda jami'an biyu suka yi musayar ra'ayoyi game da hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen biyu, da kuma batun sake gina kasar bayan ricikin da ya faru.
Zeidan ya ce, Libya tana martaba dangantakar da ke tsakaninta da Sin, kuma a shirya take ta karfafa ta daga dukkan fannoni. Ya kuma bayyana fatan cewa, karin kamfanonin kasar Sin za su sake dawo wa kasar nan ba da dadewa ba, domin su shiga a dama da su a kokarin da ake yi na sake gina kasar.
A jawabinsa, Wu Sike ya ce, Sin za ta karfafa wa kamfanoninta gwiwa da su shiga a dama da su a cikin aikin sake gina kasar, kuma yana fatan kara zurfafar hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Libya daga dukkan fannoni tare da daga matsayin wannan dangantaka zuwa wani sabon matsayi. (Ibrahim)