Shugaban rundunar sojojin kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi ya sanar a ranar Laraba da takararsa a zaben shugaban kasar mai zuwa, bayanin da mutanen kasar suka jima suna jira tun bayan kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar a cikin watan Yulin shekarar 2013.
Wannan ita ce bayyanata ta karshe a gabanku a cikin kayan soja, in ji mista Sisi a cikin wata sanarwa ta kafar talabijin.
Na dauki niyyar yin murabus daga mukamina na shugaban rundunar sojojin kasar da na ministan tsaro, in ji jagoran kifar da gwamnatin Mohamed Morsi.
Ina sanar da ku da sahihiyar takarata a zaben shugaban kasa, in ji mista Sisi, tare da bayyana cewa, ya sanya kayan soja domin kasar Masar kuma zai fitar da shi domin kasar Masar. (Maman Ada)