A ranar Laraba ne kotun harkokin mulki ta kasar Masar ta dakatar da doka da shugaba Mohammed Morsi ya sanya na gabatar da zaben majalisar kasar ran 22 ga watan Aprilu, in ji wani rahoto da jaridar Al-Ahram ta buga a shafin intanet.
Kotun har ila yau ta mika wasu batutuwa guda 14, ga kotun kolin kasar dake cikin sabuwar dokar zabe.
A ranar 18 ga watan Fabrairu, kotun dokokin kasar ta ki amincewa da dokar zaben majalisar dokokin da majalisar Shura, wato majalisar dattijai ta wucin gadi ta mika mata.
Kotun ta sake mayar da kundin dokar ga majalisar ta Shura don yin gyare-gyare dangane da cewa, akwai wasu sassan dokar da suka saba da dokokin kasar wato kamar batun kaso na ma'aikata da kuma wakilcin gundumomi cikin adalci.
Bayan kwanaki uku, majalisar Shura ta yi wadannan gyare-gyare da kotun ke tsokaci kan su, kana shugaba Morsi ya amince da gyaran.(Lami)