Hukumomin majalisar dinkin duniya masu bayar da agaji guda 7, sun koka a game da tabarbarewar halin da jama'a ke ciki a Sudan da kuma Sudan ta Kudu, tare da gabatar da kira a kan kasashen duniya da su gaggauta kawo gudumuwa.
Hukumomin sun nuna damuwarsu matuka a game da gagarumin karuwar bukatun agaji a Sudan da kuma tashin hankalin da ya addabi Sudan ta Kudu da al'ummar ta.
Hukumomin MDD sun hada da hukumar samar da abinci FAO, da hukumar kula da yara UNICEF, da hukumar lafiya ta duniya WHO, da hukumar kula da 'yan gudun hijira UNCHR, da hukumar yin kaura IOM, da ofishin kula da harkokin jin kai Ocha, da kuma majalisar kula da 'yan gudun hijira ta Denmark.
Majalisar dinkin duniyar dai ta ce, matsalar yunwa da karancin abinci na matukar karuwa a inda ake fargabar matsalar da ta shafi yara dubu 500. Matsalar dai ta fi kamari a Darfur inda a nan ne barkewar sabon rikicin ya haddasa karuwar jama'ar da suka rasa muhalli na kusan mutane dubu 400 a shekara ta 2013, a inda kuma a wannan shekarar kusan jama'a dubu 200 ne suka yi asarar muhallansu.
Kawo ya zuwa yanzu a wannan shekarar, majalisar dinkin duniya da abokan huldarta sun sami kashi ukku bisa dari ne kacal, daga cikin dala mliyan 995 da ake bukata, domin gabatar da taimakon agaji a Sudan. (Suwaiba)