A ranar Lahadi ne wakilin gwamnatin kasar Sin na musamman mai kula da harkokin nahiyar Afirka Zhong Jianhua, ya yi tattaunawa da jami'an gwamnatin Sudan a Khartoum, babban birnin kasar game da hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu da kuma halin da ake ciki a Sudan ta Kudu.
Rahotanni na cewa, Zhong ya gana da mataimakin shugaban kasar Sudan na farko Bakri Hassan Salih, da kuma ministan harkokin wajen kasar, inda bangarorin biyu suka yi musayar ra'ayoyi game da dangantakar kasashen biyu da kuma batutuwan da suka shafi halin da ake ci a Sudan ta Kudu.
Jadakan kasar Sin da ke Khartoum Luo Xiaoguang, ya halarci ganawar da aka yi tsakamnin manzon na Sin da kuma jami'an gwamnatin Sudan din. (Ibrahim)