Shugabannin kasashen Sudan da Sudan ta Kudu sun shawarci juna a ranar Lahadi kan matakan sake bude rijiyoyin man fetur a jihar Unity dake Sudan ta Kudu, makonni kadan bayan Juba ta karbe wannan jihar daga hannun 'yan tawaye, a cewar kafofin watsa labarai na kasar Sudan.
Ministan man fetur na Sudan Makawi Mohamed Awad da takwaransa na Sudan ta Kudu Stephen dhieu Dau sun gana da juna a ranar Lahadi a birnin Khartoum, tare da jaddada muhimmancin man fetur ga kasashen biyu.
Ministan man fetur na kasar Sudan ta Kudu ya isa ranar Lahadi a birnin Khartoum domin tattaunawa kan sake bude rijiyoyin daga yankunan da Juba ta karbe daga hannun 'yan tawaye dake goyon bayan tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar, in ji wadannan kafofi.
Tattaunawar ta rataya kan hanyoyin da za'a bi wajen taimakawa kamfanonin man fetur dake fuskantar matsaloli barkatai a kasar Sudan ta Kudu, musammun ma a jihar Unity, in ji ministan man fetur na kasar Sudan ta Kudu.
A nasa bangare, ministan man fetur na Sudan ya nuna cewa, kasarsa a shirye take domin biyan duk wasu bukatun Sudan ta Kudu kan sake tafiyar da ayyukan samar da man fetur domin moriyar kasashen biyu.
Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir da takwaransa na Sudan ta Kudu Salva Kiir Mayardit sun yi wata ganawa a Juba a makon da ya gabata domin tattauna matakan da za'a dauka wajen kare gine-ginen man fetur a Sudan ta Kudu.
Haka kuma hukumomin Khartoum sun amince da tura kwararru 900 domin taimakawa Sudan ta Kudu tada aikin gine-ginen samar da man fetur a wannan kasa. (Maman Ada)