Mahukuntan kasashen Sudan da na Sudan ta Kudu, sun jaddada muhimmancin aiwatar da yarjejeniyar tsaron hadin gwiwa, da bangarorin biyu suka rattabawa hannu a shekarar 2012.
Ministan tsaron kasar Sudan ta Kudu Kuol Manyang ne ya bayyana hakan, jim kadan bayan ganawar sa da shugaba Omar Al-Bashir a birnin Khartoum, fadar mulkin kasar Sudan. Yayin ganawar tasu a ranar Laraba 19 ga wata, Manyang ya mikawa Al-Bashir sakon shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir Mayardit.
Da yake tsokaci kan wannan ziyara da Manyang ya kai birnin Khartoum, ministan tsaron kasar Sudan Abdul-Rahim Mohamed Hussein, cewa ya yi, bangarorin biyu sun tattauna muhimman batutuwan da suka shafi ci gaban su, ciki hadda batun tsaron iyakoki, da aiwatar da yarjejeniyar hana jibge sojoji, a yankunan da aka kebe cikin jarjejeniyar birnin Addis Ababa. Da ma dalilan da suka kawo wa yarjejeniyar tarnaki.
A watan Maris din shekarar 2012 ne kasashen biyu, suka cimma matsayar inganta tsaron iyakokinsu, yarjejeniyar da ta hada da kebe yankunan kan iyaka da aka haramta jibge soji, domin kaucewa zaman dar dar tsakanin kasashen biyu. (Saminu)