Kasar Sudan ta sake jaddada matsayinta a ranar Litinin na ganin an maido da kwanciyar hankali da cimma kudurin kawo karshen ricikin Sudan ta Kudu ta hanyar yin shawarwari, idan ba haka ba, yakin zai iyar haddasa munmunan sakamako.
Sudan ta bayyana matsayinta na nuna goyon baya ga Sudan ta Kudu wajen samar da zaman lafiya da cimma kudurin da zai taimaka wajen sasanta bangarorin dake gaba da juna ta hanyar shawarwari, in ji ministan harkokin wajen Sudan Ali Karti a gaban manema labarai bayan dawowar shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir daga kasar Sudan ta Kudu.
Shugaba al-Bashir ya isar wa takwaransa na Sudan ta Kudu Salva Kiir muhimmin sako kan cewa, ya kamata a kawo karshen yaki domin fara shawarwarin sulhu, saboda cigaba da gwabza yaki zai iyar tura kudancin kasar cikin rashin tsaro, in ji mista Karti.
"Mun shawarci 'yan uwanmu na Sudan ta Kudu da su warware rikicinsu ta hanyar tattaunawa tare da nuna cewa, manufar Sudan ita ce ganin cewa, Sudan ta Kudu ta samu zaman lafiya da gwamnati mai karfi a Juba, wadda za ta iyar tafiyar da harkokin kasar yadda ya kamata." in ji ministan harkokin wajen Sudan.
Haka kuma jami'in ya kara da cewa, "Muna cikin kungiyar raya gwamnatocin gabashin Afirka wato IGAD da kuma tawagar sasantawa ta wannan kungiya dake gudanar da muhimman ayyuka a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, tare da karyata zancen cewa, ziyarar al-Bashir a Juba wani mataki ne na kasarsa ba wai na kungiyar ba.
A karshe ya bayyana cewa, Sudan na goyon bayan bangarorin biyu a Sudan ta Kudu da su fara shawarwari ba tare da wani sharadi ba. (Maman Ada)