in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron EU da Amurka ya bukaci gyaren fuska a cikin gwamnatin Ukraine
2014-03-27 11:07:41 cri

Shugaban kasar Amurka Barack Obama, shugaban dattawan tarayyar Turai Herman Van Rompuy da shugaban kwamitin tarayyar Turai Jose Manuel Barroso sun bukaci a ranar Laraba da a gudanar da wani gyaren fuska a cikin gwamnatin Ukraine domin fitar da kasar daga cikin rikici bayan wani zaman taronsu a birnin Brussels.

Sun nuna kwarin gwiwa ga hukumomin Kiev da su tabbatar da cewa, an kawo gyaren fuska a cikin gwamnatin kasar da ta bayyana arzikin kasar baki daya domin kare 'yancin kananan kabilun kasar.

Shugabannin uku sun watsi da komawar Crimea cikin Rasha, tare da yin kira ga hukumomin Moscow da su kaddamar da nagartattun shawarwari tare da Kiev domin bullo da bakin tsaren wannan rikici.

Duk wasu matakai da Rasha za ta dauka domin janyo tabarbarewar rikici a Ukraine na hadarin janyo wani karin sakamako mai muni, kuma mafi girma a cikin dangantakar tsakanin Rasha da Amurka da kuma tarayyar Turai ta fannin tattalin arziki, in ji wadannan shubagannin a cikin wani sabon kashedi.

A cikin sanarwarsu ta hadin gwiwa, mista Obama, Van Rompuy da Barroso sun shawarci da a kafa wata dangantakar yammacin kan harkokin waje da siyasar tsaro. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China