Kungiyar tarayyar Turai EU ta sanya wa wasu mutane 21 da ake ganin suna da hannu wajen shirya zaben raba gardamar da aka yi a yankin Crimea. Matakin da kungiyar ta ce ya haifar da barazana ga 'yancin kasar Ukraine.
Kungiyar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa bayan kammala taron ministocin harkokin wajenta a ranar Litinin.
Kungiyar ta kuma yi kira ga kasar Rasha da ta dauki matakan da suka dace, don kashe wutar fitinar da ke faruwa, kana ta fara tattaunawa kai tsaye da gwamnatin Ukraine. (Ibrahim)