in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kungiyar G7 sun ce kofa a bude take ta warware rikicin Ukraine
2014-03-25 10:01:02 cri

Shugabannin kungiyar G7 da na tarayyar Turai sun ce, har yanzu akwai damar dakile ci gaban rikicin siyasar kasar Ukraine.

Shugabannin sassan biyu sun bayyana hakan ne a jiya Litinin, cikin wata sanarwar da suka fitar, bayan ganawar da suka yi a birnin Hague na kasar Netherlands.

Har wa yau sanarwar ta bayyana kiran da shuwagabannin suka yiwa Rasha, na hawa teburin shawara domin warware takaddamar da ake yi, kan batun komawar yankin nan na Crimea karkashin ikon ta.

Ko da yake a hannu guda, sanarwar ta jaddada aniya kara daukar matakan matsin lamba ga Rashan, muddin dai ta ki karbar tayin da ake mata.

Bugu da kari shugabannin kungiyar ta G7 sun ce, ba za su halarci taron kungiyar G8, da a baya aka shirya gudanarwa a birnin Sochin kasar ta Rasha ba, a maimakon hakan za su sake zama karkashin inuwar G7 cikin watan Yuni mai zuwa a birnin Brussels. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China