Shugaban kasar Amurka Barack Obama, ya sanar da sanya wa jami'an kasashen Rasha 7 da na Ukraine 4 takunkumi, bayan da aka kammala kada kuri'ar raba gardama a yankin Crimea.
Fadar gwamnatin Amurka ta White House, ta bayyana cewa, takunkumin da gwamnatin Amurka ta sanya wa jami'an 11 da take kallo a matsayin wadanda ke da hannu wajen yiwa kasar Ukraine barazana, sun hada da hana su taba kadarorinsu da kuma yin tafiye-tafiye.
Daga cikin wadanda aka sanya wa takunkumin sun hada da hambararren shugaban kasar Ukraine Viktor Yanukovych, mataimakin firaministan kasar Rasha Dmitry Rogozin, Vladislav Surkov da Srgey Glazyev masu yiwa shugaba Vladimir Putin hidima.
Shugaba Obama ya ce, ya yi imanin cewa, za a iya yin amfani da hanyar diflomasiyar wajen warware matsalar ta Ukraine, ta yadda zai dace da moriyar kasashen Rasha da Ukraine baki daya.
A ranar Litinin ne majalisar dokokin yankin Crimea ta ayyana 'yancin kan yankin, bayan da sakamakon kuri'ar raba gardamar da aka kada ya nuna cewa, kashi 96.77 ma al'ummar yankin sun zabi koma wa kasar Rasha.
Amma kasashen yamma ciki har da Amurka, Faransa, Jamus da Burtaniya, sun ce, kuri'ar haramtacciya ce, kuma ta saba wa dokar kasar Ukraine. (Ibrahim)