Rundunar 'yan sanda a jihar Borno dake arewa maso gabashin tarayyar Najeriya ta ce, wasu mahara sun hallaka jami'an ta 5, lokacin da suka jefawa motar da 'yan sandan ke ciki bam.
Da yake karin haske don gane da aukuwar lamarin, kakakin rundunar a birnin Maiduguri Gideon Jubrin, ya ce, baya ga 'yan sandan su 5, su ma maharan su uku dake cikin wata mota kirar Golf sun mutu nan take, bayan da motar da suke ciki ta kama wuta, sakamakon fashewar bam din da suka jefa.
Har wa yau Jubrin ya ce, wata motar ta daman ta tarwatse, kusa da wata gona dake kan titin Bama zuwa Maiguduri, motar da 'yan sandan suka ce ita ma shake take da ababen fashewa.
Baya ga wadannan fashewa da ake zaton magoya bayan 'yan kungiyar Boko Haram ne suka kaddamar, an samu rahoton harbe mutane 5, da maraicen ranar Litinin, sakamakon harin da 'yan Boko Haram din suka kai kauyen Zaragajiri dake yankin Mafa. An ce, maharan sun budewa al'umma wuta, tare da kone gidaje kimanin 75.
Jihar Borno dai na shan fama da hare-haren 'yan Boko Haram, tun cikin shekarar 2009, inda maharan kungiyar ke kai farmaki a wuraren taruwar jama'a, ciki hadda mujami'a, da gine-ginen jami'an tsaro, makarantu da kauyekan jihar. (Saminu)