in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Benin za ta shirya wasannin sada zumunci karo na 22 na kwamitin wasannin motsa jikin Afrika a Mayu
2014-03-25 10:33:24 cri

Kasar Benin za ta karbi bakuncin wasannin motsa jiki karo na 22 na gasar sada zumunci na yanki na biyu na kwamitin wasannin motsa jikin Afrika (CAA) daga ranar 9 zuwa 11 ga watan Mayu mai zuwa, a wani labarin da ya fito daga kungiyar wasannin motsa jiki ta kasar Benin (FBA).

Wannan gasa na hada a ko wace shekara 'yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle kusan 60 na kasashe shida da suka hada da Benin, Burkina Faso, Mali, Nijar, Cote d'Ivoire da Togo.

Gasar sada zumunci, wata gasa ce da shugabannin kungiyoyin wasannin motsa jikin yawancin kasashen yammacin Afrika suka bullo da ita domin taimakawa wajen kara kwarewa da kwazon 'yan wasan kasashen, ta yadda za su iyar samun nasarori a yayin manyan wasannin kasa da kasa da na shiyya-shiyya, in ji mataimakin shugaban kungiyar FBA, Aristide Kotanou a wata hirarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua. Gasar ta wannan shiyya za ta gudana a filin wasan Charles De Gaulle dake Porto Novo, babban birnin siyasa na kasar Benin. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China