in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shirin bunkasa sana'o'i a karkara a Benin ya samu taimakon Sefa biliyan 15.3
2014-01-13 11:01:16 cri

Asusun kasa da kasa kan bunkasa aikin noma na FIDA ya samar da taimakon kudi na dalar Amurka miliyan 30.6 kwatankwacin Sefa biliyan 15.3 ga kasar Benin domin tallafa mata wajen ciyar da shirinta na ba da tallafi ga bunkasa sana'o'i a yankunan karkara (PAPSFRA), in ji sanarwar gwamnatin kasar a ranar Lahadi a birnin Cotonou.

Sanarwar ta ce, taimakon na FIDA ya rabu zuwa biyu, kashi 50 cikin 100 a matsayin bashi, sannan kashi 50 cikin 100 a matsayin kyauta, kowane ya tashe zuwa Sefa biliyan 7.65.

Makasudin da ake cimma ga wannan shiri, a cewar wannan snarwa, shi ne taimakawa wajen rage kangin talauci a yankunan karkara na kasar Benin ta hanyar kyautata da inganta bisa dogon lokaci kan samar da hanyoyin taimakawa kanana da matsakaitan masana'antun noma da wasu sana'o'in noma a yankunan da wannan shiri ya shafa.

A cewar wasu bayanan da suka shafi wannan dangantaka, a tsawon shekaru talatin, asusun FIDA ya zuba kudi kan tsare-tsaren ayyuka kimanin 11 bisa jimillar kudin na dalar Amurka milyan 114.2.

Haka kuma sanarwar ta nuna cewa, muhimmin burin dangantakar FIDA tare da kasar Benin shi ne na taimakawa wajen kafa hanyoyin da suka dace ga cigaban tattalin arziki a fannoni daban daban, rage kangin talauci a yankunan karkara, da kuma magance matsalar karancin abinci ga al'ummomin dake cikin hadari. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China