in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Interpol ta tabbatar da an yi amfani da fasfo biyu na sata a shiga jirgin Malaysia MH 370
2014-03-10 11:08:18 cri

Hukumar 'yan sanda ta duniya, Interpol a ranar Lahadin nan ta tabbatar da cewar, akwai fasfo biyu a cikin wadanda aka shigar da rahoton bacewa ko sace su a rajistan su, da aka yi amfani da su wajen shiga jirgin saman Malaysia da ya bace MH 370 tun ranar Asabar. Fasfo din daya na 'dan Austria ne, dayan kuma na 'dan kasar Italiya, suna cikin wadanda aka sanar da bacewar su ko sace su a kasar Thailand a shekara ta 2012 da 2013, in ji sanarwar hukumar.

Tun a wannan lokacin, in ji hukumar kasashen biyu, ba su yi wani bincike ko neman wadannan fasfo da suka bace ba, har zuwa lokacin da aka yi amfani da su na shiga wannan jirgi, don haka ba za a iya tantance ko sau nawa aka yi amfani da wadannan fasfo ba wajen shiga jiragen sama ko kuma tsallaka kan iyakokin kasashe da su ba.

Hukumar ta yi bayanin cewa, yanzu haka tana tuntuba hukumomin a wadannan kasashe domin a gano ainihin wadanda suka yi amfani da wadannan fasfo din domin shiga jirgin na Malaysia da har yanzu ba'a san inda yake ba.

Kundin ajiye bayanai na hukumar 'yan sandar ta duniya da aka kirkiro shi tun a shekara ta 2002 sakamakon harin ranar 11 ga watan Satumba na Amurka yana da nufin taimaka wa kasashe su kare kan iyakokinsu, sannan su kuma kare al'ummarsu daga harin 'yan ta'adda da sauran miyagun mutane da ke amfani da takardun bogi.

Jirgin saman Malaysia mai lamba MH 370, samfurin 777-200 yana dauke da ma'aikatan jirgin 12 da fasinjoji 227 da suka hada da Sinawa 154 lokacin da aka kasa ganin shi a sararin samaniya tun daga cibiyar lura da zirga-zirgar jiragen saman Subang ta kasar Malaysian a safiyar Asabar. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China