in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A shiga rana ta tara na aikin neman jirgin saman kasar Malaysia
2014-03-17 09:59:13 cri

Yanzu an shiga rana ta tara na aikin bincken jirgin saman kasar Malaysian nan da ya yi batan dabo, inda aka kartata ga wasu sabbin wuraren da ake ganin jirgin ka iya dosa.

Ministan sufuri na kasar Malaysia Hashimuddin Hussein ya shaida wa manema labarai cewa, ana matukar bukatar bayanan tauraron dan-adam da na na'urar da ke sadarwa da jiragen saman da kuma jiragen ruwa wajen gudanar da wannan aiki.

A ranar Asabar ne aka sanar da sabbin wuraren da za a karkata don gudanar da aikin binciken neman jirgin, wanda suka hada da iyaka daga kasashen Kazakhstan, Turkmenistan zuwa arewacin Thailand da kuma wanda zai fara daga kasar Indonesia, har zuwa kudancin tekun Indiya.

Kasar ta Malaysia tana kira ga kasashen da ke da tauraron dan-adam, ciki har da kasar Amurka, Sin da Faransa da sauransu, da su kara samar da bayanan tauraron dan-adam da za su taimaka wajen karade wadannan wurare a kokarin da ake na gano wannan jirgi.

Kimanin kasashe 25 ne yanzu haka suka shiga aikin neman wannan jirga da ya bace yau kusan sama da mako guda ke nan. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China