Babban sifeton 'yan sandan kasar Kenya David Kimaiyo, ya alkawarta samar da cikakken tsaro ga rayukan jama'ar kasar, duk kuwa da barazanar hare-haren ta'addanci da ta zamowa kasar babban kalubale.
Kimaiyo ya bayyana hakan ne a jiya Lahadi, biyowa bayan harin da wasu 'yan bindiga suka kai wata coci dake Likoni a kudancin birnin Mombasa. Harin da ya sabbaba mutuwar mutane 4, tare da jikkata wasu mutanen 17.
A halin da ake ciki dai, rundunar 'yan sandan yanki ta fara aiwatar da bincike kan musabbabin kai harin. Har ila yau rundunar ta ce, ta samu nasarar dakile wasu hare-haren da 'yan bindiga ke aniyar aiwatarwa. Bayan da ta cafke wasu 'yan ta'adda dauke da tarin ababen fashewa a birnin na Mombasa.
A ranar Lahadi 23 ga watan nan ne dai wasu mahara su biyu, suka budewa wasu masu ibada wuta a cocin ta Likoni, suka kuma tsere kafin isar jami'an tsaro wurin.
Hakan dai na zuwa ne, a daidai lokacin da al'ummun dake makwaftaka da iyakar Kenya da kasar Somaliya ke zaman dar dar, sakamakon hare-haren da masu tada kayar baya ke shiryawa, hare-haren da ake kallo a matsayin huce haushin matakan soji, da dakarun hadin gwiwar kungiyar AU ke kaiwa mayakan kungiyar Al-Shabaab, ta 'yan kaifin kishin Islama. (Saminu)