in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Kenya ya alkawarta baiwa harkar tsaro karin kulawa
2014-03-07 10:02:28 cri

Shugaba Uhuru Kenyatta na kasar Kenya, ya ce, gwamnatinsa na shirin fidda wani sabon tsarin inganta ayyukan hukumomin tsaron kasar. A wani mataki na karfafa ikon su, na fuskantar dukkanin wani kalubalen tsaro, ciki hadda na 'yan ta'adda da ka iya tunkarar kasar.

Shugaba Kenyatta ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis, lokacin da yake gabatar da jawabi, gaban kusoshin gwamnatinsa, yayin wani taron inganta makamar aiki dake gudana a Nanyuki. Ya ce, za a kara yawan kudaden da ake kebewa harkokin tsaro, ta yadda jami'an tsaron za su samu damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Karin matakan da za a dauka domin inganata harkar tsaron, a cewarsa, sun hada da horas da ma'aikata, da samar da ababen hawa, da kayan aiki na zamani, da kuma gina gidaje ga jami'an tsaron.

A nata tsokaci, sakatariyar tsaron majalissar zartaswar kasar Raychelle Omamo, jinjinawa wannan aniya ta gwamnati ta yi, tana mai cewa, matakin zai karfafa burin kasar, na kare ikon kai da martabarta.

Kasar Kenya dake gabashin nahiyar Afirka dai, na fuskantar kalubalen tsaro, musamman yakin da take yi da 'yan tada kayar baya a yankunan gabar tekunta, da kuma mayakan kungiyar Al-Shabaab ta Somaliya mai alaka da Al-Qaida. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China