Shugaba Uhuru Kenyatta na kasar Kenya, ya kara fadada ayyukan sojojin kasar na murkushe barazanar tsaro a kasar da ke gabashin Afirka.
Ma'aikatar tsaron kasar ce ta sanar da hakan cikin wata sanarwa da ta bayar, inda ta bayyana cewa, shugaba Kenyatta ya bullo da wata sabuwar runduna a karkashin rundunar tsaron kasar ta Kenya (KDF), wadda za ta rika sa-ido kan batutuwan da suka shafi fataucin miyagun kwayoyi, barazanar da ake fuskanta daga 'yan ta'adda, da yaduwar kananan makamai.
Sanarwar ta ce, an kafa sabuwar rundunar ce, sakamakon barazanar da kasar ke fuskanta sakamakon wanzuwar ayyukan ta'addanci, fataucin miyagun kwayoyi, yaduwar kananan makamai, aikata manyan laifuffuka da sauran su wadanda ke kara yaduwa a birane, kamar Nairobi, babban birnin kasar.
Gwamnatin kasar Kenya, ta shirya daukar matakan ne bayan aukuwar harin ta'addancin ranar 21 ga watan Satumba da ya faru a Nairobi, inda 'yan sanda suka bullo da yin snitiri a hanyoyin shigowa kasar domin magance matsalar tsaro.(Ibrahim)