in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Kenya ya dauki niyyar karfafa ingancin tsaro
2013-10-21 13:55:49 cri

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya dauki alkawari a ranar Lahadi cewa, zai karfafa ingancin tsaro da kuma kare kasar daga duk wata barazana daga waje.

A cikin jawabinsa zuwa ga 'yan kasar a yayin bikin ranar jarumai, shugaba Kenyatta da kasarsa ke fama da barazanar tsaro daga mayakan kungiyar Al-Shabaab ta kasar Somaliya, ya yi kira ga jama'ar Kenya da su kasance cikin shiri domin fuskantar barazanar ta'addanci.

Kasar Kenya za ta cigaba da yin daga a waje da iyakokinta, domin karfafa tsaronta, in ji shugaban kasar Kenya.

Mista Kenyatta ya bayyana cewa, akwai ayyukan kisa dake kawo fargaba a kasar Kenya, kuma ya jaddada cewa, gwamnatinsa za ta kasance cikin ko ta kwana da kuma samar da kayayyaki ga jami'an tsaro, ta yadda za su gudanar da aikinsu da dakile duk wasu ayyukan ta'addanci da tashe-tashen hankali. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China