in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar da Michelle Obama za ta kawo kasar Sin na da matukar amfani
2014-03-18 10:55:33 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei, ya ce ziyarar da uwar gidan shugaban kasar Amurka Michelle Obama za ta kawo nan kasar Sin, a ranar 20 zuwa 26 ga wata na da matukar muhimmanci.

Mr. Hong, wanda ya bayyana hakan a jiya litinin, yayin taron manema labaru da aka saba gudanarwa, ya bayyana cewa ziyarar, za ta taimaka wajen bunkasa fahimtar juna, da sada zumunci a tsakanin kasashen biyu.

Madam Michelle za ta kawo ziyara nan kasar Sin ne, bisa gayyatar da uwar gidan shugaba Xi Jinping, wato madam Peng Liyuan ta yi mata.

Game da hakan, Hong Lei ya bayyana cewa, yayin ziyarar, madam Peng Liyuan za ta gana da Michelle Obama a birnin Beijing. Sa'an nan Michelle Obama za ta kai ziyara biranen Xi'an da Chengdu.

Hong Lei ya kara da cewa, ziyarar ta Michelle Obama ta dace da lokacin da kasashen Biyu, ke kokarin kafa sabuwar dangantaka tsakaninsu. Kuma Sin na fatan ziyarar za ta samu cikakkiyar nasara. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China