0124murtala
|
Babban darektan hukumar Hisba ta jihar Kano Dr. Abba Sufi ya tabbatar da hakan ne a cikin wata zantawa da yayi da kamfanin dillancin labaran kasar ta Najeriya wato NAN a Kano.
Dr. Abba ya ce, dukkanin giyan an kwace su ne daga hannun dillalai gami da sauran jama'a a cikin kananan hukumomi 44 na jihar ta Kano.
A cewar Dr Abba, shekara ta 2013, muhimmiyar shekara ce ga hukumar Hisba saboda ta lalata kwalaben giya da dama. Ya ce, bisa dokar da aka kafa a shekara ta 2001, dukkan ayyukan da suka shafi shan giya, da saye da sayar da ita, da samar da ita, da kuma yin jigilarta,an haramta su a jihar Kano.
Har wa yau kuma, Dr. Abba Sufi ya ce, hukumar Hisba ta cafke mata masu yin karuwanci guda 66 a cikin makwanni biyu da suka gabata a Kano.
Game da harkar bara a kan titunan Kano kuwa, Dr. Abba ya ce, gwamnatin jihar ta kafa wani kwamiti mai mutane 100, a wani kokari na karfafa dokar hana bara a kan tituna a jihar.
Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.